Sarkin Karaye dake Jahar Kano ya sanar da dakatar da Abdullahi Sa’adu, Dagacin Kauyen Butu-Butu dake karamar hukumar Rimingado a Jahar Kano bisa laifin sayarwa Fulani fili. Jaridar the Cable ta ruwaito
Masarautar Karaye na daya daga cikin Masarautu hudu da gwamanan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samar a shekarar 2019.
Mai Martaba Ibrahim Abubakar shine Sarkin Karaye.
KARANTA:- Babbar Sallah: Hukumar NSCDC ta baza jami’an ta 1,750 domin tabbatar da tsaro
Haruna Muhammed Gundumawa, mai magana da yawun Masarautar shine ya bayar da sanarwar tsige Dagacin a ranar Juma’a.
Kamar yadda ya bayyana “Su dai fulanin sun zo sun fara gina Masallaci ba tare da bin ka’idar kauyen ba, wanda haka ya janyo rikici tsakanin su da mutanen Kauyen.”
“An dakatar da Dagacin ne domin samun damar isasshen bincken kan yadda lamarin ya auku.”
Shidai Hakimin Rimingado Auwal Ahmad Tukur (Magajin Rafin Karaye? ya rubutu takardar korafi zuwa ga Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar kan abunda Dagacin ya aikata.
Sarkin Karayen Ibrahim Abubakar ya tura Habibu Umar Madakin Shamaki, daya cigaba da Jagorantar Kauyen da bincike kan yadda lamarin ya auku.
Sarkin Karayen Ibrahim Abubakar yayi kira ga Mutanen Butu-Butu da su baiwa Habibu Umar hadin kai wajan jagoranci da kuma bincike.
A wani labarin Babbar Magana: Zan maka Buhari kotu idan bai ba Yan Najeriya damar rike AK47 ba, Inji wani Lauya
Wani mai fafutukar kare hakkin Dan adam Malcolm Emokiniovo Omirhobo, ya sha alwashin maka shugaban Kasa Muhammadu Buhari kotu matukar bai baiwa Yan Najeriya damar rike AK47 don kare kansu. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta.
Omirhobo, a wata wasika da ya aika a ranar 8 July, 2021, inda yayi mata laqabi da “Neman bada damar sayen bindiga kirar AK47 tare da harsashi.”
Ya bukaci shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya amince ga dukkanin Dan kasa ya mallaki bindiga kirar AK47 don kare kansa da gidansa da iyalansa harma da kayayyakinsa kan Yan ta’adda.
A lokacin da yake zantawa da Jaridar Daily trust cewa yayi ya shirya tsaf don tunkarar shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kotu nan da yan kwanaki kadan masu zuwa.
Ya kara da cewa “Ni dan Najeriya ne mai kishin kasa, kuma lafiyayye wanda yasan mai yakeyi, Ni mutum ne mai kyakykyawan dabi’a an sanni sama da shekaru biyar ban taba aikin ta’addanci ba.”