Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, ya sake dawo da Alhaji Aminu Dan Agundi Masarautar Kano a matsayin Sarkin Dawaki Babba bayan shekara 17 da tsige shi a matsayin Sarkin Dawakin Maitutu.
Mashawarcin Gwamna Abdullahi Ganduje na musamman kan harkokin masarautun gargajiya, Tijjani Mailafiya, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin.
A cewarsa, gwamnatin jihar Kano ta samu sako daga Masarautar Kano na neman dawo da Dan Agundi.
Mailafiya ya ce Sarkin ya sake dawo da Dan Agundi ne duk da mahaifinsa, Ado Bayero, ne ya tsigeshi.
A cewarsa, ana irin hakan ne don sulhunta irin rikicin dake cikin masarautar, wanda ya ce an dade ana gwabzawa a kotu.
Ya ce sake dawo da Dan Agundi cikin Masarautar da kuma bai wa Babban yayan Sarkin, Sunusi Lamido Wamban Kano na nuna cewa yanzu masauratar ta dauki wani sabon salo.
Mailafiya ya ce: “Eh, mun samu wani sako na sake dawo da Dan Agundi masarauta a matsayin Dawaki Babba, kuma nan bada jimawa ba, gwamnati za ta mayar da kyakkyawar martani don abu ne mai kyau a jihar.
A cewarsa, gwamnati na farin ciki da wannan dabarun na Masarautar na yin sulhu.
Da Lamido Bayero ne Ciroman Kano amma yanzu an nada shi a matsayin Wamban Kano.
Mailafiya ya ce gwamnati za ta amince da nadin nasu saboda an yi haka ne don ciyar da masarautar jihar gaba ne.
Ya ce gwamnati za ta amince ne sannan ta dawo da maganar doka don samun madogara.