Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi sabbin nadin makamai guda biyu a matsayin Sarkin Bai da Walin Kano.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Bashir Mahe Bashir Wali shi ne Walin Kano na bakwai da ya gaji mahaifinsa Mahe Bashir Wali wanda yake raye amma kwanan nan ya yi murabus saboda ya nayin tsufa da rashin lafiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Ma’aikatan Majalissar Dokoki Sun Baiwa Gwamna Wa’adin Biyan Hakkokin Su
Mansur Mukhtar tsohon ministan kudi kuma mataimakin shugaban bankin cigaban musulunci a halin yanzu shine Sarkin Bai na tara tun bayan jihadin Usman Danfodio da ya gabatar da tarihin masarautar Kano.
Mahaifinsa, kafin rasuwarsa, shi ne mafi dadewa a Majalisar Masarautar Kano, tun lokacin da aka kafa masarautar a karni na 19.
Ya yi shekaru 63 a matsayin hakimin gunduma, shugaban ‘yan majalissar Sarki da kuma mai zabar sarki kafin ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.
Da take zantawa da manema labarai, matar farko ga sabon Sarkin Bai, Hadiza Mansur, ta yi addu’ar Allah ya yi masa jagora.
“Yau tarihi ne a rayuwarmu. Muna addu’ar Allah ya kai shi wannan matsayi, Ya ba shi damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, ya kuma yi masa jagora a kan haka. Muna yi wa duk wanda suka zo fatan komawa gida lafiya daga wurare daban-daban.”
Bikin nadin rawani ya samu halartar shuwagabannin gargajiya da na siyasa da na al’umma daga masarautu ciki da wajen jihar Kano.
A wani labarin kuma, An Garkame Tsohon Jami’in MDD A Gidan Yari Bisa Laifin Ta’ammali Da Kwayoyi Don Yin Fyade Ga Mata
An yanke wa Karim Elkory, tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da ya yi wa wata mata fyade, hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.
An gudanar da ayyukan ne tsawon shekaru goma yayin ayyukan jin kai zuwa kasashe daban-daban.