Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda a jihar Zamfara Alh. Muhammad Ahmad Asha rasuwa bayan shekara 16 a gadon sarauta.
Sarkin ya rasu ne da safiyar Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya, kamar yadda wani na kusa da fadar Ƙaura Namoda ya tabbatar wa BBC.
Amma Sarkin ya dade yana fama da hawan jini da kuma ciwon suga.
Babu dai wani cikakken bayani kan dalilin rasuwarsa.
Shi ne Sarki na biyu a tarihin sarautar Sarki mai sanda ta Emir mai daraja ta ɗaya a Ƙauran Namoda bayan mahaifinsa, amma shi ne Sarki na 16 a masarautar Kiyawan Ƙauran Namoda.
Sarkin ya rasu yana da shekara 71 a duniya, kuma ya bar mata uku da ƴaƴa.