Sabon Kontagora Mohammed Barau Kontagora ya karɓi takardar naɗin shi a matsayin Sarki daga Gwamnan Jahar Niger Abubakar Sani Bello a ranar Juma’a.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Gwamnatin Jahar ta fitar a ranar Juma’a, wanda ya bayyana cewar bayar da takardar ya wakana a gidan Gwamnatin Jahar.
Daya samu wakilcin Kwamishinan Ƙananan hukumomi da cigaban Al’umma da kuma harkokin Masarautu Emmanuel Umar, Gwamnan ya shawarci sabon sarkin daya yi dukkanin abinda zai iya domin bunƙasa zaman lafiya a yankin sa, domin bunƙasa tattalin arziki da samar da cigaba.
KARANTA WANNAN LABARIN: IPOB: A halin yanzu Sojoji sun miƙa mana Chiwetalu Agu — Cewar DSS
A sanarwar mai taken “Gwamna Abubakar Sani Bello ya gabatar da takarda ga sabon Sarkin Masarautar Kontagora Alhaji Mohammed Barau, Gwamnan ya yabawa Al’ummar yankinsa, inda ya buƙace su dasu marawa shugaban su baya.
Sanarwar ta naƙalto gwamnan na cewar “Na godewa Allah ga Al’ummar Masarautar Kontagora wanda suka yarda da gwamnati, tare da bin dukkanin wasu hanyoyi har ya zuwa wannan lokaci.
“Duk da yazo a lokaci mai wahala, ina addu’a ga Allah daya albarkace shi, da samar da zaman lafiya a yankin sa.”
A lokacin da yake karɓar takardar, sabon Sarkin ya godewa Allah daya naɗa shi a matsayin Sarki na bakwai na Masarautar Kontagora.
An dai zaɓi sarki na bakwai (Sarkin Sudan) a ranar Lahadi 19 ga watan Satumba na shekarar 2021 a Kontagora, kamar yadda dokar data kafa masarautar ta tanada.
Naɗin sabon Sarkin ya biyo bayan mutuwar Mai Sudan Alhaji Saidu Namaska, wanda ya rasu a ranar 9 ga watan Satumba na shekarar 2021, bayan shafe shekaru 47 a saman karagar mulki
Comments 1