Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abukakar III, ya yi Allah-wadai da rashin isasshen jari a fannin kiwon lafiya a Najeriya, inda ya yi kira ga daidaikun jama’a da su saka hannun jari a harkar donmin bunkasa ta.
Ya bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da makarantar Hill College of Nursing Sciences mai zaman kanta a Jos, babban birnin jihar Filato.
Sultan wanda ya samu wakilcin mai martaba Sarkin Dass, Othman Bilyaminu Othman, ya ce ya zama wajibi masu hannu da shuni su tallafa wa kwalejin.