Sarkin Musulmi yayi Allah Wadai da Kisan Harira da ɗiyan ta, ya buƙaci a kamo wanda suka aikata
Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III yayi Allah Wadai kan kisan Harira Jibrin da ƴaƴa 4 a Isulo ta Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa ta Jahar Anambra da ƴan IPOB suka yi.
Sultan wanda shine Shugaban Ƙungiyar Jama’atul Nasril Islam yayi Allah Wadai da wannan mummunan lamari, yana mai bayyana kisan a matsayin rashin hankali da tuni.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babu Wata Shaida Dake Nuna Yan Takarar Jam’iyar APC Na Baiwa Deleget Kudade—– Abdullahi Adamu
Muna kira ga Gwamnatin Tarayya data tashi tsaye wajen zaƙulo ƴan Ta’addan IPOB daga inda suke ba tare da ɓata lokaci ba.
Sultan yayi Allah Wadai da kisan rashin rashin imani da yawaitar kashe-kashe na Ƙasa a dalilin rashin tsaro.
Sanarwar tace “Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto Muhammad Sa’adu Abubakar, yayi Allah Wadai da kisan Harira Jibrin, mace mai ciki da ɗiyan ta guda 4 a Isulo na Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa ta Jahar Anambra.
“Wannan ƙari ne bisa ga yawaitar kisan mutane da dama, musamman musulmi a yankin Kudu maso Gabas ta Najeriya.
“Wannan ta’addancin yana ƙirƙirar ƙiyayya. Yanzu Lokaci ne da Gwamnati ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki.”