By Abbas Yakubu Yaura
Wani Sarkin Oyo, Oloko na Oko, Oba Gbariel Adepoju, ya rasu ranar Lahadi yana da shekaru 85 a duniya.
Har ya zuwa rasuwarsa ya yi sarauta a wani garin Oko Ile da ke karamar hukumar Orire a jihar Oyo, kamar yadda gidan rediyon Najeriya ya rawaito.
Marigayin kafin rasuwar ya kasance mai son yiwa al’ummar sa hidima da kuma kwatar musu ‘yancin su musamman ma idan na sam zai danne na kasa dashi.
Oba Adepoju ya hau gadon sarautar kakanninsa ne a shekara ta 1997 kuma ya bi sahun kakanninsa da sanyin safiyar Lahadi.
Manyan sarakuna uku a jihar sun shude tsakanin Disambar shekarar 2021 da Janairu 2022.
Soun of Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewumi shima yabi sahun kakanninsa a ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2021 yana da shekaru 95.
Olubadan na Ibadan land, Oba Saliu Akanmu Adetunji ya rasu a ranar 2 ga watan Janairun 2022 yana da shekaru 93 a duniya.