Allah Ya yi wa Sarkin Rano rasuwa a ranar Asabar da yamma a asibitin Nasarawa da ke jihar Kano.
Alhaji Tafida Abubakar Ila ya rasu ne bayan gajeriyar jinya, yana da shekara 74, kamar yadda Kabiru Ado Rurum, dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano da Bunkure kuma Turakin Rano ne ya tabbatar wa BBC labarin rasuwar.
Mai magana da yawun Masarautar Ranon Wali Ado ya ce Sarkin ya yi jinyar kwana biyar ne, inda aka kai shi asibiti a jiya Juma’a.
Yana daga cikin sarakuna hudu masu daraja ta daya na sababbin masarautun jihar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira a bara.
Wali Ado ya ce dama Sarkin yana da cutar hawan jini da ciwon suga da ke taso masa lokaci-lokaci.
Za a sanar da lokacin da za a yi jana’izarsa nan gaba kadan, a cewar Fadar Ranon.