Sarkin Zazzau, Dr Shehu Idris ya taya sabon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Farfesa Kabir Bala murnar kasancewarsa sabon shugaban Jami’ar wanda zai kwashe wa’adi guda na tsawon shekara biyar.
Shugaban tawagar fadar masarautar Zazzau din, Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmadu Fatika shi ne ya mika takardar taya murna din ga Farfesa Kabir a yayin da suka kai masa ziyara a ofishinsa dake cikin Jami’ar.
Alhaji Abbas Ahmadu Fatika ya ce masarautar ta Zazzau na taya shi murna bisa wannan mukamin shugabantar Jami’ar Firimiyan Arewa.
Inda shugaban tawagar ya yi masa addu’a da nufin Allah ya taimake shi a wannan mukamin na shi domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
A na shi jawabin, Farfesa Kabir Bala ya nuna jindadinsa bisa wannan ziyarar, inda ya yi alkawarin ya yi aiki tukuru wajen bunkasa alakar dake tsakanin Jami’ar da Masarautar Zazzau. Sannan ya mika gaisuwarsa ta musamman ga Sarkin Zazzau, da kuma alkawarin bayar da gudummawa da kuma neman shawara daga Sarkin zuwa ga hukumomin Jami’ar.
Takardar taya murnar dai, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Dr Shehu Idris ne ya sanya mata hannu da kansa.