Rahotani daga fadar mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahamdu Bamalli, ya bayar da umarnin gaggawa dakatar da hakimai guda hudu daga masarautar sa.
Dakatawar gaggawar ta hadar da Garkuwan kudun Zazzau Alhaji Mohammadu Sani Uwais da Uban-garin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris da Wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo da Sarkin Dajin Zazzau Alhaji Shehu Umar.
Kafin yanzu rahotanni sun tabbatar da cewar an soki tubabbun hakiman da saɓa doka ta uku da ke cikin kundin laifukka da hukunce-hukuncen hawa a Masarautar Zazzau wadda ta haramta wa kowane hakimi yin hawa da ƴan tauri riƙe da makamai.
Wannan dai wani mataki ne da masarautar ta dauka domin Bin umarnin gwamnatin jihar wajen tabbatar da zaman lafiya