Tsohon dan Wasan gaba na Kasar Holand Marco Van Basten ya bukaci mahukunta a fagen kwallo da su kawar da dokar hura satar gida wato offside, inda ya ce kwallo ba tare da offside ba zai fi dadi matuka.
An yi ta samun rudani a harkar kwallo tun bayan bullowar Na’urar dake taimakawa alkalin was was wato VAR inda ake ganin akwai bangareanci yayin busa offside.
Hukumar dake kula da hukunci kan kwallon kafa ta duniya ta ce za ta ci gaba da nazari kan shawarwari da aka bayar kan wannan matsala ta offside kamar irin wanda tsohon kcoin Arsenal Arsene Wenger ya bayar kan dabarun baiwa dan wasan gaba wata dama ta kara kaimi.
“Gaba daya hankali na bai kwanta ba kan wannan doka ta busa satar gida, ni a gani na kwallon kafa zai fi kayatarwa idan aka ce babu wannan doka” cewar Van Basten wanda ya tyaba rike mukamin Daraktan Wasanni naFIFA a shekarar 2016 zuwa 2018 ya ce.