Wata kotun majistare da ke Surulere a jihar Legas, a ranar Juma’a, ta yanke wa wani matashi dan shekara 23, Mai suna Ibrahim Salisu, daurin watanni shida a gidan yari, saboda satar kadarorin coci da ya kai na naira 300,000.
Alkalin kotun, Misis M. I. Dan-Oni, ta yanke wa Salisu hukunci ne, bayan ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi na sata.
Dan-Oni, wanda bai bayar da zabin biyan tara ba, ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin ne, tare da aiki mai wahala.
Wanda ake zargin, wanda ke zaune a gida mai lamba 9, a kan Titin Seriki St, na yankin Idi-Araba, dake jihar Legas, an gurfanar da shi ne tun a ranar 9 ga watan Yuli shekarar nan, bisa zargin laifin sata.
KARANTA WANNAN LABARIN: GWAMNATIN Tarayya ta ai’yana Talata a Matsayin Ranar Hutun Edil Maulud
Jami’in Dan sanda Mai gabatar da kara, Insfecta Courage Ekhueorohan, ya bayyanawa kotun cewa, Salisu ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Yunin shekarar nan, a Cocin Deeper Christian Life Ministry, dake Daura da Aina Street, na yankin Surulere, dake Legas.
Ya ce Salisu ya shiga cocin ya sace manyan tukwane na aluminium guda uku, kwanon soye-soye, kujerun zama guda biyar, kwanon aluminium guda biyu, da mumbari biyu, duk darajarsu ta kai Naira 300,000.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, sata ta sabawa sashe na 287 na dokar manyan laifuka na jihar Legas, 2015.