Wata malama mai shekaru 22 tana hannun hukuma bayan an kama ta dumu-dumu ta yi lalata da wani dalibinta, LIB ta ruwaito.
Ashley Waffle, wata malamar wucin gadi a makarantar gwamnati ta Granite, ta fara aiki ne ranar 10 ga watan Oktoba, daga nan ta fara hira ta Snapchat da dalibinta mai shekaru 16 a ranar 25 ga watan Oktoba, wanda makwanni 2 kenan da fara aikinta.
KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta baiwa ɗalibin da yafi kowa makin jamb tallafin karatun miliyan 3
Sai dai an samu labari a waje cewa jami’an makarantar sun sanar da ‘yan sanda abin da ke tsakanin Waffle da dalibinta bayan maganar ta fara yawa a gari.
Kamar yadda takardar kotu ta nuna, an ga waffle da yaron har sau biyu a dakinta kafin ranar 9 ga watan Nuwamba.
An fatattake ta a ranar 10 ga watan Nuwamba kasancewar ana zargin abin da tayi zai iya da ayi mata daurin shekaru 15 a gidan yari.
Yanzu haka tana gidan gyaran halin yankin Greer a kulle. An samu rahoto kan yadda iyayen yaron su ke bayar da hadin kai dari bisa dari ga jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da bincike.
Ƴan Ƙungiyar Asiri sun harbe Ɗalibi har lahira a Kwalejin Yabatech
An harbe wani dalibin kwalejin fasaha ta Yaba da ke Legas a ranar Alhamis da yamma da misalin karfe 9 na dare, wanda ake zargin ɗan kungiyar asiri ne ya harbe shi har lahira.
Wakilinmu da ke makarantar a lokacin da lamarin ya faru, ya lura da cewa an harbi dalibar har sau biyu yayin da sauran daliban suka gudu domin tsira.
Wata daliba mai suna Tayo Aina ta bayyana cewa tana bayan dalibar da aka harbe.