A karon farko Kasar Saudi Arabiya ta tabbatar da bullar sabon nau’in annobar cutar Coronavirus ta Omicron a kasar ranar Laraba, wanda aka yi imanin shi ne na farko da aka samu rahoton a cikin kasashen Larabawa.
An gano lamarin a cikin wani dan kasar Saudiyya da ya dawo daga wata kasa da ke Arewacin Afirka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya ruwaito, inda ya ambato wani jami’in ma’aikatar lafiya.
Sai dai Jami’in lafiyar bai ambaci sunan kasar ba.
Tun da farko dai kasar Saudiyya mai arzikin man fetur ta haramta zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasashen Afirka da dama saboda fargabar yaduwar sabon nau’in na Omicron.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ware nau’in cutar Omicron a matsayin “tafi kowace hadari” ta Hukumar Lafiya ta Duniya, a cikin fargabar cewa yana iya yaduwa, ko da yake da yawa ba a bayyana ba.
dpa/NAN