Rahotanni sun bayyana cewa Cristiano Ronaldo da abokiyar zamansa Georgina Rodriguez za su karya doka a kasar Saudiyya ta hanyar zama tare duk da dokar kasar da ta hana masoyan da ba su yi aure ba kwana wuri guda.
Dan wasan dan kasar Portugal mai shekaru 37, ya koma kungiyar Al-Nassr ne a watan da ya gabata bayan ficewar sa daga Manchester United kuma rahotanni sun ce zai rika karbar fam miliyan 175 a shekara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bidiyo: Yadda Baƙuwa Ta Rika Taba Wa Amarya Wuraren Albarkatunta a Wurin Biki Ya Ja Hankali
An bayyana shi a ranar Talata 3 ga watan Janairu, a gaban magoya bayan sa 25,000 a filin shakatawa na Mrsool a Riyadh, zuwa wurin wasan wuta.
Iyalan Ronaldo ma sun kasance a filin wasan inda aka bude shi kuma kafar yada labarai ta SPORT ta kasar Sifaniya ta bayyana cewa ta hanyar zama da Rodriguez masoyan za su karya dokar Saudiyya.
Rodriguez da Ronaldo ba su yi aure ba tukuna, a zahiri za su saba wa dokar Saudiyya.
Sai dai rahoton na SPORT ya ci gaba da cewa, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar Sipaniya EFE, saboda matsayin Ronaldo na daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi kasuwa a duniya, da wuya a hukunta dan wasan na Portugal.
A yayin da yake tsokaci kan wasu lauyoyin Saudiyya guda biyu, kwararrun lauyoyin sun yi tsammanin hukumomin da abin ya shafa ba za su shiga halin da Ronaldo ke ciki ba.
Wani ya ce: ‘Ko da yake har yanzu dokokin sun haramta zama tare ba tare da aure ba, amma hukumomi sun fara rufe ido ba sa tsananta wa kowa. Tabbas, ana amfani da waɗannan dokokin ne lokacin da akwai matsala ko kuma wani laifi.’
A wani labarin kuma,2023: Kano Ta Shirya Fadakarwa Ga Mahajjata Masu Neman Zuwa Makka
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta ce ta shirya shirin wayar da kan alhazai na duk mako a cibiyoyi 16 na mahajjata na shekarar 2023.
Sakataren zartarwa na hukumar, Ambasada Muhammad Abba-Danbatta, a wani taron manema labarai a Kano ranar Alhamis, ya ce za a fara shirin ne a tsakiyar watan Janairu.