Rahotanni daga Saudiya sun ce an jiyo kara mai karfin gaske a sassan birnin Riyadh, wadda da rundunar sojin kasar ta ce ta wani makami mai linzami ne da ta tarwatsa, bayan da mayakan Houthi suka yi yunkurin kaiwa birnin na Riyadh farmaki.
Cikin sanarwar da ta fitar, rundunar sojin Saudiya tace jumillar makamai masu linzami 6 ta tarwatsa, wadanda ‘yan tawayen na Houthi suka harba daga Yemen zuwa wasu biranen kasar ta Saudiya baya ga Riyadh.
Dakile yunkurin kai farmakin da mayakan na Houthi suka yi, na zuwa ne sa’o’i bayan kazamin fadan da ‘yan tawayen suka gwabza da sojojin Yemen a birnin Ma’arib, inda akalla mayaka 50 suka rasa rayukansu daga bangarorin biyu.
Har yanzu dai mayakan na Houthi basu dauki alhakin harba makaman masu linzami kan Saudiya ba, sai dai a baya sun sha yin ikirarin kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki kan wasu yankunan kudancin kasar, baya ga yunkurin farwa birnin Riyadh a lokuta da dama.