Ministan albarkatun man fetur na kasar Saudiyya, Yerima Abdul’aziz bin Salman ya ce kasar za ta dakatar da rabin man fetur din da take fitarwa a rana sakamakon harin da ‘yan tawayen Houthi dake kasar Yemen suka kai wa cibiyoyinta na mai da ke Abqaiq da kuma Khurais a safiyar ranar Asabar.
Ministan ya ce adadin man da kasar za ta daina fitarwa zai kai ganga milyan 5 da dubu 700 a rana.
Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi Iran a matsayinta na kasar da ke taimaka wa ‘yan tawayen na Houthi da hannu wajen kai wannan hari, yayin da a wata zantawa ta wayar tarho, shugaban Donald Trump ya ce Amurka za ta taimaka wa kasar ta Saudiyya domin kare cibiyoyinta na mai.