Ma’aikatar shari’a ta kasar Saudiyya ta haramta aure a kasa da shekaru 18. Inda ta ayyana shekaru 18 a matsayin shekarun da za a iya aure kadai.
Ministan shari’a kuma shugaban majalisar shari’a ta kasar, Sheikh Walid Al-Samaani shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya aikawa dukkanin kotunan kasar wannan sabuwar dokar.