Kasar Saudi Arabia ta kafa dokar hana yan kasar ta zuwa kasashe uku ciki hsr hadaddiyar Daular Larabawa wato Dubai.
Kasar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne don rage yaɗuwar cutar korona ta Covid-19.
Wannan doka ta zo ne makonni uku bayan da kasar Saudiyyar mai arzikin man fetur a duniya ta ɗage dokar hana fita bayan da aka yi wa rigafin cutar ta korona, dokar da ta shafe shekara guda tana aiki.
Da ma dai kasar hadaddiyar Daular Larabawar ita ce kasa mafi girma ga Saudiyya da ta zamo mata matattarar yawon bude ido.
Yanzu haka kasashen da Saudiyyar ta Haramta wa yan kasarta shiga sun hada da Habasha da Vietnam sai kuma kanta makociyarta wato Dubai.