Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta kasa ta fitar da tsarin yadda matafiya za su sayi tikitin jirgin ƙasa ta intanet.
Matafiya dai a yanzu sun samu saukin tafiya daga Kaduna zuwa Abuja ko kuma daga Abuja zuwa Kaduna ta jirgin ƙasa, inda yanzu za su iya shiga Intanet kawai su sayi tikitin su daga gida ba tare da bin layi a tashar jirgi ba.
Tun a baya, jama’a da dama masu bin jirgin sun sha ƙorafi ga gwamnatin ƙasar da ta fito da tsarin da zai sauƙaƙa siyan tikitin jirgin, inda akasari suka bayar da shawara a koma sayar da shi ta intanet.