A ranar Litinin ne wata kotun sauraren manyan laifuka dake Ikeja ta yankewa Rasak Abiona hukuncin kisa, biyo bayan dukan mahaifinsa dan shekaru 62 a duniya da karfen rodi wanda yayi sanadin mutuwarsa har lahira.
Kamfanin dillancin labarai NAN ya bayyana cewa Rasak ya samu rashin jituwa da mahaifin nasa ne akan wasu kadarori.
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo bayan sauraren hujojji ta bayyana cewa wanda ake zargi da aikata laifin, ya amsa laifinsa a yayin da yake hannun’Yan sanda amma daga baya a kotu ya musunta hakan, kuma ya kasa kawo wanda zasu kare ikirarinsa na cewa mahaifinsa ya rasu tun da dadewa.
Mai shari’ar ta yankewa Rasak hukuncin kisa bayan da aka kama sa da laifi karkashin sashi na 221 na kundin laifuka na shekarar 2011 na jihar Legas.
https://dimokuradiyya.com.ng/kotu-ta-yankewa-wani-malamin-addinin-kirista-hukuncin-kisa/
Ta ce “abin takaici ne ace da ya kashe mahaifinsa”.
“Ko shakka babu duk wanda zai daki mutum da karfen rodi a kai tabbas yayi shirin lahanta mutum ne”. Cewar mai shari’a Taiwo.
Ta kara da cewa “wannan yana daga cikin illar saurin fushi da mutane ke yi a lokuta da dama”.
“Dan haka wannan kotu ta yankewa Rasak hukuncin kisa, sakamakon kashe mahaifinsa da yayi”.