Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, APC, Adamu Garba, ya dage cewa sake fasalin naira wata makarkashiya ce ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu. Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.
Garba ya ce babban bankin Najeriya, CBN, ya sake fasalin naira ne domin wata makarkashiya ce ta hana Tinubu zama shugaban Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Sake Fasalin Kudi; El-Rufai, Yahaya Bello Sun Isa Kotun Koli
A wani sakon da Garba ya wallafa a shafinsa na twitter, ya rubuta cewa: “Ko ta yaya kuke son gani, wannan sabon tsarin naira na CBN da aka bullo da shi a lokacin zabe wani shiri ne na hana Bola Ahmed Tinubu zama shugaban Najeriya.
“Ta yaya kuma za ku iya bayyana wannan aikin tada hankali a cikin wannan lokacin? yaya? In sha Allahu wannan makircin ma zai yi nasara ba!”
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya tabbatar da kalaman Garba.
Shugaban majalisar ya ce da alama makircin ya ci tura domin har yanzu ‘yan Najeriya na ci gaba da rike amana da jam’iyya mai mulki da Tinubu duk da halin da suke ciki.
“Ba wanda zai iya gamsar da ni cewa ba makirci ba ne na hana Asiwaju [Tinubu] zama shugaban kasar nan.” Inji shi.
A wani labari kuma, Tabbatar Da Kyakkyawan Zaɓe, Manyan Ayyuka Ne Na Sojoji GOCs, Da kwamandoji
Babban hafsan soji, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya umarci dukkanin kwamandojin Janar (GOCs) da sauran kwamandoji su tabbatar da yanayi mai kyau da tsaro a zaben 2023.
Yahaya ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake kaddamar da aikin tabbatar da zaman lafiya a dukkan bangarori da sassan kasar nan