By Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun jihar Adamawa karkashin jagorancin babban alkalin jihar Nathan Musa, ta haramtawa hukumar zabe mai zaman kanta gudanar da zabe a mazabar Michika.
Ficewar dan majalisar wakilai daga jam’iyyar PDP, Ayuba Kwada zuwa jam’iyyar APC, ya janyo cece-kuce a majalisar dokokin jihar.
Bayan sauya shekar Kwada, kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Aminu Iya-Abass, ya ayyana kujerar dan majalisar a matsayin wadda babu kowa akai.
Sai dai kuma umurnin da mai shari’a Musa ya bayar na wucin gadi tare da hana akanta janar na jihar dakatar da biyan albashin dan majalisar har sai an saurari karar da kuma yanke hukuncin karshe.
Kwada, wanda aka fi sani da ‘Depolis’, ya shigar da karar mai lamba HC/ADSY/73/2022, ya roki kotu da ta ci gaba da bin doka da oda kafin bayyana kujerar sa ba bisa ka’ida ba, har sai an kammala fassarar sashe na 109 karamin sashe (1g) na Kundin Tsarin Mulki na shekarar 1999 da sauraron karar akan sanarwa.
Babban Alkalin jihar, a hukuncin da ya yanke nafarko a ranar Alhamis din da ta gabata bayan ambato karar, ya bayar da umarnin wucin gadi da ya haramtawa hukumar INEC aiwatar da duk wani mataki da zai kai ga gudanar da zabe a mazabar Michika ta jihar Adamawa.
Mai shari’a Nathan Musa ya kara da cewa kotun ba za ta iya tantance haramcin ayyana kujerar Depolis ba a wannan mataki kamar yadda aka ambata.
Ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 16 ga watan Mayu, 2022, domin cigaba da sauraren shari’ar.
Karar mai lamba HC/ADSY/73/2022, ta sanya Ayuba Kwada a matsayin wanda ya shigar da kara, yayin da kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, kwamishinan kudi, Akanta Janar na Jiha, PDP da kuma INEC ke cikin wadanda ake kara na 1 zuwa 6.
Comments 1