By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Kwara ta bayyana kujerar dan majalisa mai wakiltar mazabar Ojomu/Balogun na karamar hukumar Offa, Hon. Saheed Adekeye Popoola a matsayin wanda babu kowa.
Popoola, wanda kwanan nan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP daga jam’iyyar APC wanda ya kasance babban jigo ne ga ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed.
Duk da cewa har yanzu Lai na cikin jam’iyyar APC, bangaren jam’iyyar a jihar Kwara masu biyayya ga ministan sun fice daga jam’iyya mai mulki.
Shugaban jam’iyyar SDP na jihar, Mista Lekan Alabi, ya tabbatar wa Jaridar Daily Trust ta wayar tarho cewa an fara tattaunawa tsakanin jam’iyyar da kungiyar ta balle.
Kakakin majalisar, Engr Yakubu Salihu Danladi, yayin da yake bayyana matakin da majalisar ta dauka a zamanta na ranar Alhamis, ya bayyana cewa sanarwar ta yi daidai da tanadin sashe na 109 (1)G na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Ya yi nuni da cewa ya kamata Popoola ya bar kujerar sa ta wakilcin mazabar Ojomu/Balogun na karamar hukumar Offa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada bayan ya fice daga APC zuwa SDP.
Ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa dan majalisar ya fice daga APC zuwa wata jam’iyya.
Kakakin Majalisar Danladi ya gabatar da cewa saboda haka majalisar ta sanar da kwamishinan zabe na jihar game da ci gaban da aka samu.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai, Popoola ya ce matakin da majalisar ta dauka ya zama abin raini.
“Shugaban majalisa da majalisar duka ba su da ‘yancin bayyana kujerata ko ta kowane mamba, har ma da INEC. Kotu ce kawai za ta iya yin hakan.
“Na ba su umarnin kotu daga babbar kotun jihar Kwara a jiya (Laraba) na mika wa ofishin shugaban majalisar na hana su daukar irin wannan matakin amma duk da haka sun ci gaba. Yanzu haka lamarin yana tsakanin su da kotu,” ya kara da cewa.