By Ishaq Dabai
Masu ruwa da tsaki a bangaren gwamnati da kungiyoyi masu zaman kan su sun bayyana cewa, sauyawa matasa tunani ita ce hanyar da za a bi wajen dakile safarar bil’adama.
Masu ruwa da tsakin da suka hadar da hukumar yaki da safarar bil’adama ta najeriya NAPTIP, da hukumar wayar da kai ta kasa NOA, da kungiyar yan kasuwa, masana’antu da ma’adanai da harkar noma NACCIMA da shugabanin gargajiya, sun gudanar da wani taro don tattaunawa a dakin taro na kungiyar kula da shige da fice ta IOM, kuma anan ne suka bayyana hakan.
Taron yace dole ne a samar da wasu damarmaki madadin yin hijira zuwa wani waje.
Yayin da yake jawabi shugaban hukumar NAPTIP Mr Aganran yace ”dukkanin mu iyaye ne kuma dukkanin mu ‘yan kasa daya ne ya kamata mudakile masu safarar bil’adama, idan muka rage zamu samu saukin hatsarin yin shijira a ayan kunanmu.”
Shima a nasa bangaren daraktan NAO ya baiwa matasa shawarar cewa su daina yadda wani yana yaudarar su, da sunan zai kaisu Amurka, ko wata ƙasa.
Kazalika shugaban NACCIMA, Barista Kola Awe ya sanar da muhimmanci gane shekaru da cewa “kada kayi la’akari da lnda kake rayuwa a matsayin ka na matashi, wajen jin gwanda ka bar muhallin da kake, kana bukatar ka tsaya ka tsara wajen da kasamu hanyar da zaka gaiyato wasu.