Tsohon Sarkin Kano na 14 kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasa (CBN), Alhaji Muhammadu Sanusi, ya bukaci ‘yan Najeriya da su goyi bayan tsarin Kashles da shugaba Buhari ya bujiro da shi. Daily trust ta rawaito.
A wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta a ranar Litinin, Sarki Sanusi ya bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan, domin gujewa fadawa hannun bara gurbin yan siyasa.
KU KARANTA: Sauya Fasalin Naira: Gwamnonin APC 3 Sun Gana Da Ministan Shari’a
Ya kara da cewa manufar ba sabuwa ba ce, yana mai cewa an shafe sama da shekaru goma ana aiwatar da ita.
Da yake sukar ’yan siyasa, Sanusi ya ce manufar ta mayar da abin da suka wawushe dukiyar da ba ta da amfani.
”Wannan manufa (manufofin sake fasalin naira) an shafe sama da shekaru 10 ana aiwatarwa.”
”Kuma Najeriya ta isa wajen amfani da tsarin tun da muna da hanyar mu’amala ta musayar kudi.”
A wani labarin kuma: An Sake Samun Girgizar Kasa A Turkiyya
Girgizar kasa mai karfin maki 6.4 ta afku a kudancin kasar Turkiya.
Ta afku ne makonni bayan da wata mummunar girgizar kasa ta yi barna a yankin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 46,000.