Kungiya mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta SERAP, ta ce ta kai ƙarar shugaban kasa Buhari kotu ne akan abin da ta kira “kasa bincikar ɓacewar Naira biliyan 3.8 da aka ware wa hukumomin kiwon lafiya.”
BBC Hausa sun wallafa cewa “Sanarwar ƙungiyar mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktan ta Kolawole Oluwadare ta ce ta shigar da ƙarar ne a babbar kotun Abuja inda take neman kotun ta tilastawa shugaban binciken kuɗaɗen da suka ɓata da kuma magance girman matsalar rashawa a ma’aikatar lafiya da asibitocin Tarayya da kuma Hukumar da ke sa ido a kan abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC”.
Hukumar ta SERAP ta yi gargadin cewa, “Rashin binciko zargin da ake yi na ɓatan kuɗaɗen na kiwon lafiya, da gurfanar da wadanda ake zargi da laifi a gaban kotu, ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya marasa ƙarfi cikin mummunan hatsarin kiwon lafiya, wanda ya saɓa wa tsarin mulki da ƴancin dan adam a dokar ƙasa da ƙasa da kuma alƙawalin da aka yi wa ƴan Najeriya yaƙi da rashawa.”
Zuwa yanzu hukumar SERAP ta ce kotu ba ta tsayar da ranar sauraren ƙarar ba.