Gwarzuwar yar wasan Tennis ta duniya da ta lashe kyautar zinare har sau huɗu a gasar Olympic wato Serena Williams, ta tabbatar da cewa yanzu kam fa ita ta yi bankwana da gasar Olympic na birnin Tokyo a wannan shekara.
Williams mai shekara 39 yar asalin kasar Amurka wacce kuma ta fara wasan Tennis a shekara ta 2000, ta tabbatar da wannan matsaya tata ne a yayin wani taro gabannin fara wasanta na Wimbledon a ranar Lahadi.
” Magana ta gaskiya babu suna na a jerin sunayen yan wasan Olympic na bana, ban san kuma da hakan ba, domin da na sani lallai da zan fafata”
Sai dai da aka tambayi Williams taki zurfafa bayanai dangane da wannan mataki.
Yar wasan wacce ta lashe gasar Grand Slam har sau 23 ta ce babu ta yadda za a yi tayi wasa da rayuwar ƴar ta mai shekara 3 a duniya ta hanyar kaita cikin dandazon jama’a.