• Serena Williams ta yi Ritaya bayan andoke ta a gasar Wimbledon.
• Takasa Kamo Abokiyar Hamayyarga wato Margret Courts.
• An yi tunanin Serena Williams zata iya lashe gasar Wanda aka cire ta a jiya Talata.
Fatan Serena Williams na yin kan-kan-kan da Margret Courts, wajen lashe gasar Wimbledon na mutum dai,-dai karo 8 ya ci karo da cikas, biyo bayan doke ta da aka yi a wasan zagayen na Wimbledon a jiya Talata.
‘Yar kasar Belarus Aliaksandra ce, ta doke Williams Yar kasar Amurka mai shekaru 39, wacce ta yi fatan lashe gasar, domin kai wa mataki iri daya da Margret courts, wajen lashe manyan gasar Tennis sau 24 wato (Grand slam).
A wasan da suka fafata a zagayen farko, ta fara da kafar dama da ci 3-1 sai bayan dawowa zagaye na biyu Aliaksandra sasnovich ta mai da wasan 3-3, kuma a karshe ta saka Williams kuka a gaban magoya bayan ta.
Ana ganin cewa Serena Williams, na da damar lashe gasar na Wimbledon a wannan shekarar, biyo bayan dakatar da manyan abokan hamayyar Simona Halep da Naomi osaka daga gasar, duba da dukkannin su, Sun ta ba lashe gasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Matawalle ya zama Shugaban Jam’iyar APC na Zamfara
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Williams, ke kokarin murmurewa da kuma shirin tunkarar gasar US open a watan satumba, wacce ta taba lashewa karo 6, ko daya ke rabon da Serena Williams ta babbar gasar Tennis Tun a shekarar 2017 data lashe Australia n Open.
A karshe hakan dai Williams ta sanar da yin ritayan ta daga wasan Baki daya.