
- Sergio Ramos ya bar kungiyar Real Madrid
- A jiya ne kwantiragin Sergio Ramos ya kare da kungiyar Real Madrid bayan ya shafe shekaru sha shida a ƙungiyar
- Shuwagabannin Real Madrid da Ramos ba su amince a kan sabunta kwangilarsa ba
Ɗan wasn bayan zai tashi daga kungiyar da ya yi shekara 16 yana wasa
Kungiyar Real Madrid ta bada sanarwar cewa Sergio Ramos zai tashi daga kulob din. Sanarwar ta fito ne a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni, 2021.
Ga abin da sanarwar da ta fito daga shafin yanar gizon kungiyar take cewa:
“Za a kira taron manema labarai a ranar Alhamis, inda za a sanar da tashin kyaftin din Real Madrid bayan shekaru 16
KARANTA:- Gasar cin kofin Ingila sun fidda jadawalin wasannin shekarar 2021/2022
Sagio Ramos dai lokacin da yake bugawa Real Madrid ne Ramos ya ci gasar Euro har sau biyu a kasar Sifen. Haka zalika tauraron ya ci kofin kwallon Duniya a shekarar 2010.
Bayan zamansa kyaftin, Ramos mai shekara 35 ya na da kwallaye fiye da 100. Ba kasafai ne aka saba ganin ‘dan wasan baya mai irin wadannan tulin kwallaye ba.
A shekarar bana, Ramos bai buga wasanni da dama ba saboda rashin lafiya. Hakan ya jawo har ya gagara zuwa gasar cin kofin Turai wanda ake yi a kasar Hungary.
Dazu kun samu rahoton yadda Cristiano Ronaldo ya yi sanadiyyar da kamfanin Coca Cola ya yi asara, bayan tsohon ‘Dan wasan na Real Madrid ya ki shan lemun.
Yayin da aka shirya taron ‘yan jarida, sai aka ajiye wa Ronaldo da kocin Portugal robobin lemun Coca Cola a gabansu, shi Ronaldo sai ya dauke na sa daga gabansa
Comments 1