Dan wasan Spain Sergio Ramos, mai shekara 33, ya bukaci Shugaban Real Madrid Florentino Perez da ya bar shi ya koma China, kamar yadda kafar yada labarai ta (LaSexta – in Spanish) ta bayyana.
Sai dai, Perez ya shaida wa gidan rediyon Spain cewa yana da kwarin gwiwar da wasan Chelsea, Eden Hazard, zai koma Madrid, a cewar jaridar (Mail).
Kocin Chelsea Maurizio Sarri ya ce ya amince ya koma Juventus inda kungiyar za ta kara masa fam miliyan 1.2 duk shekara, kamar yadda jaridar (Mail) ta ruwaito.