Kungiyar kwallon kafa ta Genoa dake Seria A ta sanar da korar Andriy Shevchenko daga kungiyar bayan ya shafe watanni biyu yana jan ragamar kungiyar.
A cikin wata sanarwa da Genoa ta fitar ta ce kocin ‘yan kasa da shekaru 17 Abdoulay Konko ne zai rike mukamin kocin na rikon kwarya har sai kungiyar ta samu wanda zai maye gurbin dan kasar Ukraine din na dindindin.
Tsohon dan wasan AC Milan da Chelsea Shevchenko ya samu nasara daya ne kawai daga cikin wasanni 11 da ya buga a dukkanin gasanni bayan da Genoa ta dauke shi aiki a ranar 7 ga watan Nuwamba, rashin nasara na baya bayan nan da kungiyarsa ta yi a hannun Milan a gasar cin kofin Italiya ranar Alhamis.
A karkashin jagorancin Shevchenko Genoa ta zira kwallaye uku kawai a wasanni tara na Seria A, ya kasa yin nasara kuma ya yi rashin nasara sau shida.
Genoa, wacce Banker 777 Partners siya a watan Satumba shekarar 2021, tana matsayi na biyu a kasan teburin gasar na Seria A, maki biyar tsakanin ta da fita cikin wadanda ka iya shiga Gasar dake kasa da Seria A.
Shevchenko ya jagoranci Ukraine zuwa wasan kusa da na karshe a gasar Euro 2020 a bazarar da ta wuce, inda Ingila ta lallasashi da ci 4-0 a birnin Rome.
.
Comments 1