Hukumar da ke kula da samar da guraben karatu a manyan makarantu (JAMB) ta bayyana cewar shafinta na yanar gizo bai lalace ba, inda ma ta shaida cewar sakamakon jarabawar da daliban da suke neman guraben karatu a manyan makarantu (UTME) wadanda suka zana na shekarar 2019 yana nan a ciki babu abun da ya sameshi. Shugaban sashin yada labarai na hukumar JAMB, Dakta Fabian Benjamin shine ya tabbatar da hakan a lokacin da ke ganawa da kamfanin dillancin labarai ta kasa a jihar Legas jiya. Benjamin wanda ke maida martani kan bayanin da ke cewa hukumar ta fitar da sanarwar manema labaru da ke shaida cewar ba su sake sakamakon jarabawar ba ne biyo bayan lalacewar da shafinsu na yanar gizo-gizo (Serber) ya yi har ma suka ce wadanda suka zana jarabawar za su sake gudanar da jarabawar. Ya ce, “Muna son mu wanke kanmu daga irin wannan shaci-fadin wadanda wasu ‘yan damfara suke yadawa, babu wani kamshin gaskiya kan wannan batun sam-sam. “Mu ba mu fitar da wani makamancin wannan bayanin manema labaru da ke cewa turakarmu ta lalace ba. Kawai wannan aikin wasu suke kokarin kawo rudani da tayar da hankulan wadanda suka zana jarabawar ne da kuma tayar wa al’umma hankula. “Ba mu yada wani abu makamancin wannan ba, mu dai mun maida hankulanmu ne wajen ganin mun cimma nasarar da muka sanya a gaba, hukumar JAMB tana kan aikin tantance jarabawar ne domin tabbatar da magance dukkanin wata magudin jarabawa daga kowace cibiyar zana jarabawa. Wannan shine dalilin da ya sa fitar da sakamakon jarabawar ya samu jinkiri,” Inji Kakakin JAMB. Babban jami’in ya ci gaba da shaidar da cewa hukumar ta kusa kammala dukkanin tantancewar da take yi, wanda za ta sake sakamakon jarabawar nan ba da jimawa ba, “Abun da muke kan kokarin yi shine dukkanin wadanda suka saba dokar jarabawar nan an tsamesu, Ina tabbatar muku cewar dukkanin wanda aka samu da saba dokar jarabawa zai fuskanci fushinmu,” A cewar shi. Mista Benjamin ya bukaci ‘yan Nijeriya da su fahimci kokarin da hukumar ke yi wajen tabbatar da magance matsalolin mutune marasa kan gado, yana mai shaida cewar ta hakan za a samu gina matasa masu cike da kyawawan halaye da kuma gina kasa, “Muna son gyara abubuwa da yawa da ake daukansu sakaka. Idan wasu ko wani na da wata hanya ta tafka munamunarsa to kasa ba za ta gyaru ba,” kamar yadda ya shaida.