Shafin YouTube mallakin Google a ranar Talata ya dakatar a asusun shugaban kasa Donald Trump da ke a shafin tare da sauke wani bidiyon da ya dora sakamakon karya dokokin shafin na tayar da zaune tsaye, biyo bayan wata zanga zanga da ta barke a cikin birnin Amurka.
Tun bayan barkewar zanga zangar da magoya bayan Trump suka haddasa a Capitol da ke birnin Washington DC a makon da ya gabata, kafofin sada zumunta suka dakatar da shafukan Trump a kafofinsu.
Masu kafofin sada zumuntar, sun yi zargin cewa Trump na iya amfani da shafukansa domin ci gaba da haddasa rikici a yayin da ake shirye shiryen rantsar da Joe Biden, bayan cin nasara a zaben kasar da ya gudana shekarar da ta wuce.
“Bisa la’akari da fargabar da ake ci gaba da yi ta tashin hankali, mun cire wani bidiyo da Donald J Trump ya dora a shafinsa, bidiyon ya karya dokokin kamfaninmu,” cewar YouTube a cikin wata sanarw.
KARANTA WANNAN: Ranar bude makarantu: An samu rabuwar kawuna tsakanin jihohi
An dakatar da shafin Trump daga dora hoto ko rubutu a YouTube har na tsawon mako daya, kamar yadda jaridar Channels TV ta ruwaito.
A makon da ya gabata ne kamfanin Facebook ya dakatar da shafin Trump da kuma shafinsa na Instagram biyo bayan rikicin da ya barke a US Capitol, wanda ya kawo tsaiko a alamta nasarar Joe Biden.
Da ya ke sanar da dakatar da shafukan Trump, shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg ya ce Trumo ya yi amfani da shafukansa wajen rura rikicin da ke faruwa a birnin Amurka, wanda hakan zai zama babbar matsala idan aka barshi ya ci gaba.
Ita kuwa kamfanin Twitter, sun ma goge shafin Trump gaba daya daga rumfunan mutane na kafar su, wanda ya kawo karshen shafinsa da ya fi kaunar amfani da shi.