Wani Likitan Hakora a Najeriya Dakta Basik Tochukwu ya bayyana tsotsan ɗan yatsa da yara ƙanana ke yi ka iya sanya kwarangwal din jikinsu ko kuma hakoransu ba za su daidaita yadda ake so ba.
Dakta Basil a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labara na Kasa NAN a birnin Jos ya shaida cewa duk wani yaro dake tsotsan ɗan yatsa to lallai na da hatsarin fama da wargajewar dasashi ko kuma Mukamukinsa ba za su kwari ba kana su daidata yadda ake bukata ba.
Bisa ga haka ne Likitan ya shawarci iyaye da su rika kwaɓar ƴaƴan su daga wannan dabi’a, don kyautata rayuwar su a nan gaba.
Ya kara da cewa kuma duk wasu iyaye da ƴaƴansu ke shan hannu kana ya gaza dainawa, to su gaggauta mika shi ga likitoci domin su kam akwai su da siddabaru bila’adadin wadanda za su yi amfani da shi wajen dakatar da yaran.