A ranar Lahadi Masana’antar Fimafiman India ta girgiza a sakamakon rasa daya daga cikin jigo kuma daya daga cikin Jaruman masu tasowa mai suna Sushant Singh Rajfur dan shekaru 34.
Rohoton fari na kar takwana na ‘Yan sanda ya bayyana cewar Singh Rajfur ya kashe kansa ne ta hanyar rataya bayan da aka sami gawar sa a gidan sa dake Bandra West dake garin Mumbai.
Rohotonnin sunce ana kyautata zaton Rajfur ya kamu ne da ciwon damuwa wato ‘depressed’ a turance. Domin a kwanukan nan ya kebe kansa kuma yana cikin gayar damuwar da ba’a fahimci musabbabinta ba.
Dama Kasa ga sati guda Manajar sa mai suna Disha Salian ta kashe kanta bayan da ta jefo kanta daga bene na hawa 14 a inda aka rankaya asibiti da ita kuma tace ga garin ku nan. Shi kan shi jarumin ya bayyana kaduwa da alhinin sa na rasuwar abokiyar aikin tasa.
Jarimin Kafin ya shiga bollywood ya fara wasu shirye shirye a TV na Kasar india inda ya sami farin jini da karfuwa harda ma kyaututtuka, haka kuma yayi wa kamfanunnuka da dama talla ta inda ya zamo fuskar sa ta zamo sannan a fadin India shiyasa koda ya fara aikin Film a Masana’antar ya zamo Karbabbe a wurin al’umma.
Ya fara ne da wani film da ya sami Karbuwa mai Farin jini mai suna ‘Kai Poche!’ A 2013 inda daga bisani ya gabatar da shahararrun Fima fiman da suka hada da Ms Dhoni, The Untold Story da kuma Detective Byomkesh Bakshy.
Tuni da manyan jarumai da Kanana suke ta aikawa da sakunan alhinin wannan rashi da shine fitattu na hudu da masana’antar ta rasa a wannan shekarar, kuma har Firamininsta Narandara Modi shima ya fitar da sakon alhinin sa a twitter.