Kotu ta Wanke Matar Abdulmalik Tanko wanda ake zargi da Kashe Karamar Yarinya Hanifa a Jahar Kano
Jamila Muhammad Sani ta tsaya a gaban ƙuliya ne a matsayin mai bayar da shaida kan tuhumar da ake yi wa mijinta da sace tare da kashe yarinyar ƴar shekara biyar a watan Janairu.
Jamila ta amsa tambayoyi daga lauya mai gabatar da ƙara, Barista Musa Lawan, inda ta yi wa kotu bayani kan abin da ta sani game da zargin ɗauke Hanifa, wacce ɗaliba ce a makarantar da ta zam mallakin mijinta Abdulmalik.
KARANTA WANNAN LABARIN:Harin Ƴan Ƙunar Bakin wake a Masallaci ya Kashe Mutane 30, da jikkata 60 a Pakistan
Ta ce ya kawo mata yarinya ta tambaye shi ina iyayenta sai ya ce da ita uwar yarinyar ta sami aiki a Saudiyya, kuma ta tafi Abuja don cike wasu takardu.
Amma har yamma na ga bai mayar da ita gida ba sai nake tambayarsa yaushe mahaifiyar yarinyar za ta dawo gida, kuma me ya sa har yanzu ba ta kira shi ba?
“Sai ya ce ba ta kira ba, daga baya sai ya ce sun yi magana da mahaifiyar yarinyar ta ce akwai layi ba za ta dawo ba a ranar ba,” in ji Jamila.
Ta ci gaba da bayyana wa kotu cewa bayan kwana biyu sai ya sake ce wa mata uwar yarinyar ta taho amma wani uzuri ya tsayar da ita a hanya, daga baya da ta sake tambayarsa, sai ya ce ta daina tambayarsa.
‘Yadda na san sunan yarinyar’
Matar Abdulmalik ta ce ta kai ga sanin sunan yarinyar ne a tsawon kwanakin farko da kai Hanifa gidan, a lokacin da take kuka, ita kuma ta rarrasheta ta haɗa ta da ‘ya’yanta biyu don yin wasa.
Ta shaida wa kotu cewa yarinyar da ke jikin wani hoto da kotu ta yi wa laƙabi da hujja ta 5 lallai Hanifa Abubakar ce.
Sannan ta ce bayan kwana uku ta sake yi wa mijin nata Abdulmalik magana ya ce kudin mahaifiyar yarinyar ne ya ƙare tana Kaduna.
Amma saboda yadda ta matsa masa, sai ya faɗa mata cewar zai mayar da Hanifa wajen babarta.
Jamila ta ƙara da cewa a daren ranar na 5 ya sanar da ita zai mayar da Hanifa gida, a lokacin ta fara bacci, ya ce a ɗauko kayan makarantarta a saka mata.
Duk da ce masa da ta yi dare ya yi a lokacin 11 na dare, amma haka ya tafi kai ta a cewarsa.
“Lokacin da ya dawo na fara bacci, na kuma tambaye shi cewar ya mayar da yarinyar gida? Sai ya ce ‘e’.
“Bayan ƴan kwanaki sai na ga wata farar waya a hannunsa, sai na tambaye shi inda ya same ta sai ya ce min ta wani Hashimu Isyaku ce ya ba shi ya saka masa caji,” kamar yadda ta bayyana
Zamu kawo maku yadda akayi kotun ta wanke ta daga zargi.
Idan Baku manta ba dai jiya ne matar Abdulmalik Tanko mutumin da ake zargi da kisan Hanifa a Kano, ta bayyana a gaban kotun shari’a Usman Na-Abba a karon farko a ranar Alhamis da safe.