Sashen Jami’an Tsaro na Farin Kaya a ranar Laraba, yabi shawarar da Babbar Kotun Tarayya ta bayar a Abuja, na ƙin rufe Dukkanin farfajiyar Kotun da Kewayen ta, gabanin shari’ar Shugaban Ƙungiyar Tsagerun Biafra Nnamdi Kanu.
Mai Shari’ar Binta Nyako wadda ta sanya ranar yau, ƙarfe 1 na rana, ta shawarci Jami’an Tsaron na DSS dasu sanar da ofisoshin su akan shawarwarin data bayar.
Duk da dai Nyako bata bayar da umarni ba tana umartar Jami’an tsaro akan lamarin, tace bazata bari harkokin Kotun a tsaida su ba.
A dubawar da akayi da sanyin safiyar yau, ya nuna cewa, Ma’aikatan Babbar Kotu, da Lauyoyi, da Ƴan Jarida, da sauran su, an basu damar zuwa har inda ake gudanar da shari’ar da kewayen ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun Kai hari Kasuwar Shanu dake Abia
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, akwai walwala na zuwa ko’ina, da ababen hawa ciki da wajen Kotun.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito cewar Joji a ranar 19 ga watan Fabrairu ta shawarci Jami’an tsaro na Farin Kaya da kada su mamaye wurin da sabon tsarin su na tsaro a Kotun, har sai zuwa ƙarfe 12 na rana.
Kotun ta bada umarni ga DSS dasu mamaye Kotun ne idan aka fara Shari’ar Kanu akan ta’addanci.
Nyako ta yi ƙorafi cewar shari’ar wasu yana shafar su duk lokacin da akace anyi shari’ar Kanu, sakamakon yawaitar jami’an tsaro da rufe hanyoyin zuwa Kotun.
Daga nan sai ta sauraron shari’ar ta’addanci ta Kanu zuwa Ƙarfe 1 domin ganin an kammala wasu shari’ar.