Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce akwai bukatar a sauya salon wajen yakin da ake yi da ‘yan ta’addan Boko Haram.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a sanarwar da Isa Gusau mai magana da yawunsa ya aike wa BBC, gwamnan ya bayyana haka ne a Fadar Shehun Borno yayin da yake jawabi a gaban Shugaba Buhari lokacin da ya kai ziyara birin Maidugurin ranar Laraba.
Buhari ya je Maiduguri ne domin mika ta’aziyyarsa bisa hare-haren da Boko Haram ta kai a Auno wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30 tare da kona motoci 18 da kuma gidaje.