By Abbas Yakubu Yaura
Amfani da muggan kwayoyi da sauran haramtattun abubuwa na kara zama ruwan dare a cikin al’ummarmu a yau, lamarin daya kara daukar hankula a Kano. Ba zato ba tsammani, wadanda suka fi fuskantar wannan barazana sune matasa. Annobar shaye shayen miyagun kwayoyi ta yi wa matasan illa ta yadda wasu daga cikinsu suka zama marasa kwanciyar hankali da rudanin zuciya.
Wani rahoto da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta fitar ya nuna cewa kashi 40 cikin 100 na matasan Najeriya wadanda suke tsakanin shekaru 18 zuwa 35 na shiga cikin muguwar dabi’ar shaye-shayen miyagun kwayoyi.A bayyane yake, shan miyagun ƙwayoyi abu ne dake buƙatar kulawar gaggawa.
Wannan ya zama dole domin mafi yawa daga cikin matasan sun fara wannan dabi’a tun suna kananun yara inda kuma a hankali suka fara sha’awarta tare da tsunduma cikin shaye shayen.
Matasan suna shaye-shayen miyagun ƙwayoyi saboda wasu dalilai da suka haɗa da rashin kyaututtukan iyaye zuwa tasirin ƙungiyar takwarorinsu.Yawancin iyaye basa kulla alaƙa da ’ya’yansu saboda suna “shagaltuwa” da aiki ko kasuwancin su, inda mafiya yawancin lokaci suna barin yaran da ƙarancin kulawa ko rashin kulawa, wanda ke sa irin waɗannan yaran su kasance cikin haɗarin shan miyagun kwayoyi.
Don haka, wannan kira ne ga masu mulki wajen farkawa zuwa tunkarar wannan babban kalubale musamman iyaye. Ya kamata iyaye su kulla dangantaka mai kyau kuma su yi amfani da lokaci mai kyau tare da ‘ya’yansu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Domin dakile wannan annoba a Kano, akwai bukatar bayar da shawarwari da hadin gwiwa tsakanin iyaye da malaman addini da jami’an tsaro su hada kai wajen yakar wannan dabi’a.