Darakta, wayar da kan jama’a, na hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP), Josiah Emerole, ya ce kashe-kashe domin yin tsafi na, kungiyoyin asiri da tashe-tashen hankula a cikin al’umma ana iya danganta su da shan muggan kwayoyi.
Ya bayyana hakan ne a Abuja Laraba a wani taron bita mai taken ‘Cutar Muggan Kwayoyi, Kisan matsafa da kuma kungiyoyin Asiri a Najeriya’ wanda gidauniyar Katolika Caritas Foundation of Nigeria, African Faith da Justice Network da Dominicans for Justice and Peace suka shirya.
Ya ce taron bitar an yi shi ne da nufin samar da cikakkiyar dabarar da za ta iya magance ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Chigbu Odemulam Chilee, Mataimakin Darakta, Rage Bukatun muggan kwayoyi, wanda ya wakilci Hukumar Yaki da fataucin miyagun Magunguna ta Kasa, ya ce: “Tsarin tarbiyyar yara, al’adu, rashin aikin yi, talauci, damuwa, rashin girman na gaba, takaici da matsi, wasu dalilai ne da ke mutane tunzura mutane shiga cikin shaye-shayen miyagun kwayoyi.
“A cikin kowane hudu daga cikin masu shan muggan kwayoyi a Najeriya, daya mace ce, kuma daya daga cikin mutane biyar da suka yi amfani da kwayoyi, na fama da matsalar shan muggan kwayoyi. Amfani da miyagun ƙwayoyi ya fi zama ruwan dare tsakanin Matasa masu shekaru 25 zuwa 39.”
Babban jami’in tsare-tsare na hukumar wayar da kan jama’a ta kasa Okechi Robinson, ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi a yanzu ya kai ga daliban sakandire, har ma da daliban firamare da shekarun su ya Kai 10.
Robinson ya ce: “Daya daga cikin hanyoyin magance matsalar ita ce ta yin hukunci mai tsauri kan laifukan miyagun kwayoyi. Mun ga irin wannan yanayin a ƙasashe kamar Singapore, Malaysia da sauran inda hukuncin ya fi tsanani ga laifukan miyagun ƙwayoyi.
“Wannan a fili ya taimaka musu wajen ragewa sosai idan ba a kawar da matsalar muggan kwayoyi ba a wadannan kasashe. Don haka Najeriya na bukatar hukunci mai tsauri don magance laifukan miyagun kwayoyi