Malamin addini musuluncin nan a Kano Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya sake yin rikici da lauyoyinsa da suke ba shi kariya ta hanyar rashin gamsuwarsa kan yadda sabbin lauyoyinsa na shi ke kare shi a kotu kan bayyana shaidu da suka gabatarwa kotu.
Rahotanni daga majiyarmu a kotun sun bayyana cewa; Sheikh Abduljabbar ya bayyana hakan ne a yayin zaman kotun na yau Alhamis da ya gudana a babbar kotun musulunci da ke kofar Kudu a birnin Kano.
A yayin zaman kotun na yau din a karkashin Alkali Ibrahim Sarki Yola, mai shari’an ya fara ne da tambayar sabbin alkalan Abduljabbar tuhume-tuhume da suka bukaci daukaka ƙara.
Umar Mohammad da ke jagorantar tawagar sabbin lauyoyin, ya ce sun sauka daga kan bukatar daukaka kara, amma suna nan kan bakar su na rashin hallacin tsayawar lauyoyin da gwamnati ta dauka masu mukamin SAN da kuma batun gabatar da sabbin tuhume-tuhume.
Sai dai Farfesa Mohammad Lawan Yusufari lauyan da ke gabatar da kara ya ce kotu na iya bayar da hukunci kan batun hallacin tsayawarsu a gaban ta.
Bayan amincewa da hakan yasa mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya bukaci masu kara da su gabatar da shaidun da aka bukace su.
Kotu a yau ta sake dage shari’ar zuwa 28 ga watan Oktoban da mu ke ciki domin sake wani zaman.