Gwamnan Jihar Yobe Kuma Kantoman Jam’iyyar APC ta Kasa Mai Mala Buni ya sha alwashin cewa Jam’iyyar tasu tana nan daram sai ta ga bayan shekara 32 a kan karagar mulki.
Idan za a iya tunawa dai a shekara ta 2008 Shugaban jam’iyyar PDP na wanchan lokacin Cif Vincent Ogbulafor ya yi makamancin wannan alwashi kan cewa jam’iyyar su ta PDP sai ta shafe shekara 60 tana mulki, amma shekara bakwai bayan wanchan cika baki ne aka tunkude su daa karagar mulki.
Da yake ƙaddamar da kwamitin Tuntuba na Jam’iyyar APC a birnin tarayya Abuja, Mai Mala Buni ya ce jam’iyyar za ta nazarci kundin tsarin mulkin ta ta inda za ta rubanya kokarin ta da zai ba ta damar gyara kura kuran ta da ta yi a baya.
“Kudurin mu a yanzu shine mu kasance a kan karagar mulki na tsawon wa’adi 6, 7 kai har ma 8 saboda nu gina Najeriya da Yan Najeriya.
A tsokacin shi yayin kaddamar da Kwamitin, Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya ce a yanzu haka jam’iyyar APC tuni ta gama shan damarar gudanar da babban taron ta na kasa wanda zai gudana a watan Yulin Wannan Shekara.
Da yake maida martani dangane da Wannan kalamai na APC, Kakakin Jam’iyyar adawa ta PDP Kola Ologbindiyan ya ce babu ko shakka za a yi waje rod da APC a Babban zaɓen 2023.
“Yan Najeriya sun zaku ma ace 2023 ya yi don sun nuna wa APC irin halin da suka tsinci kan su a ciki, Saboda su riga da sun yanke kauna kan cewa babu yadda Najeriya za ta iya rayuwa a hannun APC.” Cewar Ologbindiyan.