Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ta sake shiga cikin wani rudani na siyasa yayin da Sanata Ibrahim Shekarau, wanda ya koma jam’iyyar PDP daga NNPP wata guda da ya wuce aka amincewa da shi a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ce Shekarau ya ci gaba da zama dan takarar sanata a jam’iyyar NNPP, duk da sauya sheka zuwa PDP.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Da yake bayyana dalilin da ya sa ya bar jam’iyyar NNPP bayan watanni uku, ya ce Kwankwaso ne ya yaudare shi, inda ya ce jam’iyyar ta gaza cimma wasu yarjejeniyoyin da suka cimma kafin ya sauya sheka.
KARANTA KUMA: Batun ficewar Shekarau daga NNPP Zuwa PDP Shifcin Gizo Ne
Shekarau wanda ya taba zama gwamnan jihar Kano har sau biyu, ya koma PDP ne a ranar 29 ga watan Agusta, amma abin da ya ba mutane mamaki, a ranar Talata ne aka sanya sunansa a matsayin dan takarar jam’iyyar NNPP ta Kano ta tsakiya a zabe mai zuwa. Hukumar INEC, duk da cewa ya yi ikirarin cewa ya sanar da hukumar a hukumance kan janye shi daga takarar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Sai dai kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa INEC Festus Okoye, ya ce sanarwar ta biyo bayan cikar wa’adin, inda ya jaddada cewa Shekarau ya ci gaba da zama dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP.
Ya ce, “A tsarin jadawalin mu da ayyukan da aka fitar a ranar 26 ga watan Fabrairu 2022, 15 ga watan Yuli, 2022, an kayyade a matsayin ranar karshe na janyewa da maye gurbin ‘yan takarar Majalisar Tarayya. Ana zargin tsohon gwamnan jihar Kano ya janye takararsa ne a ranar 26 ga watan Agustan 2022.
“Ma’anarsa ita ce ya zauna kuma zai ci gaba da zama dan takarar jam’iyyar NNPP. Sunansa zai kasance a ranar zabe a matsayin dan takarar jam’iyyar NNPP a mazabarsa ta Sanata.”
Ba mu yi mamaki ba – NNPP
Da yake mayar da martani kan lamarin, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar NNPP a Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya ce jam’iyyar ba ta yi mamakin yadda sunan Shekarau ya fito a cikin jerin sunayen ba, inda ya ce jam’iyyar ta fara aikin gyara matsalar.
Rogo ya ce bisa ka’idojin da INEC ta fitar, ana sa ran jam’iyyar za ta bi wasu matakai wajen ganin an sauya sunan Shekarau.
Ya ce tun da Shekarau ya fice bisa radin kansa jam’iyyar ta gudanar da sabon zaben fidda gwani a cikin wa’adin da sabuwar dokar zabe ta tanada.
“Duk abin da muka yi shi ne cikin lokacin da aka kayyade kuma muna bin hanyoyin da suka dace. Don haka mun tattara dukkan bayanai kuma za mu shigar da batun zuwa kotu kuma bayan mun bi diddigin hujjojinmu, muna da tabbacin kotu za ta umurci INEC da ta canza sunan dan takarar da ya gabata da sabon dan takara daga gare mu. Yanzu muna jiran ranar sauraron karar,” inji shi.
Wani mai taimaka wa Shekarau kan harkokin yada labarai, Sule Ya’u Sule, ya ce duk da jadawalin da INEC ta fitar, matsayin sanatan yana nan daram.
Ya ce, “Kun san ya rubuta wa INEC cewa ya janye takararsa. An gabatar da kwafin wasikar ga jama’a; hakan ya kasance matsayinsa”.
A wani labarin kuma: Wata Mata Ta Zama Ma’aikaciya Ta Sace Jariri A Asibitin
Koyarwa
An samu tashin hankali a sashin karbar haihuwa na asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda aka ce daya daga cikin tagwayen da aka haifa ya bata.
A zantawarsa da Daily Trust, mahaifin tagwayen da aka haifa, Ibrahim Dallami Khalid ya ce wata mata ta shiga dakin da matarsa da tagwayen ke ciki ranar Laraba.