Siyasar Kano dai yanzu haka na ci gaba da daukar zafi, sakamakon yadda jiga jigan jam’iyyar ke ta kaura daga cikin ta zuwa NNPP.
Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi watsi da gayyatar da Ganduje yayi masa na ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da lokacin da Gsndujen ke kokarin hana Shekarau din komawa Jam’iyyar NNPP.
A daren jiya ne dai gwamnan Ganduje ya ziyarci gidan Shekarau da ke Mundubawa, Inda ya rikoshi da su tafi Abuja domin ganawa da shuganan kasar.
Da fari dai Malam Shekarau ya amince da gayyatar, Amma da ya gano ba shuganan kasa ne ke Kiran nasu ba, sai yayi watsi da ita.
Yanzu haka dai ido ya koma kan Sanatan, domin ganin matakin karshe da zai dauka, shin zama a APC ko kuma Kaura.