Shekaru 4 nayi ban taɓa takardar Kuɗi ba — Kanye West
Fitaccen Mawaƙi a Ƙasar Amurka, Kuma biloniya, Ɗan Kasuwa Ye da akafi sani da Kanye West ya bayyana cewar tsawon shekaru huɗu bai taɓa takardar Kuɗi ba.
A lokacin wani taron Shagali na Balenciaga SS23 a garin New York, wani bidiyo da aka nuna, an ga wata mata ta nufi mawaƙin nan na Amerika, ta nufe shi da kuɗi a hannu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin Rasha Da Ukraine Zai Durkusar Da tattalin Azrikin Duniya—- Bankin Duniya
Ya maida mata jawabi yana cewa “a’a bana karɓar kuɗi, nayi Shekaru huɗu ban taɓa kuɗi”. Masoyan sa, sun bayyana kaɗuwa akan abinda yace, suna bayyana abun a matsayin abun ban sha’awa, domin ya zama Hamshaƙin Ɗan Kasuwa.
Haka zalika, Mawaƙin ya jinkirta ranar da zai fito da Album nashi Yeezy x Gap sakamakon Ɗaukar ta a makaranta.
Comments 2