Shugaban kasa Buhari ya taya Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, murna na cika shekar 45 ya na kan gadon mulkin sarautar Zazzau.
Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Shugaban kasar ya bayyana Sarkin da Limamin zaman lafiya da kwanciyar hankali da aminci, kuma mai kawo wa al’ummarsa ci gaba.
Buhari ya bayyana cewa Sarkin na 18 a tarihin kasar Zazzau kuma shugaban Sarakunan Kaduna, haske ne kuma matattarar tarihi da al’adun masarauta.
A cewarsa, Shehu Idris, Sarki ne Mai daraja wanda gwamnatin tarayya da ta jiha ta shafe shekara da shekaru ta na amfana da shawarwarinsa na manya.