Waɗanda lamarin faɗowar na’urar gini ya rutsa dasu a lokacin hajjin shekarar 2015 a Saudi Arabia daga Jahar Kaduna, sun ce har yanzu basu karɓi wata diyya ba, bayan shekaru 6 da afkuwar lamarin.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar a ranar 11 ga watan Satumba na Shekarar 2015, wata Na’urar yin gini ta faɗo a lokacin wata tsawa mai ƙarfi a Ka’aba dake birnin Makkah, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da raunata wasu.
Najeriya ta rasa mahajjata 6 daga Gombe, da Katsina da Jahar Kaduna, a yayinda wasu suka samu raunuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: El-Rufa’i ya maganta akan cire Shugaban Ma’aikata, ya musanta sanya hannun Sarki Sanusi
Majiyoyi sun bayyana cewa Hukumomi a Ƙasar Saudiyya, tuni suka saki kuɗin a matsayin diyya ga dukkanin waɗanda suka rasu da jin raunuka a shekarar 2018.
Acewar sanarwar da ƙasar Saudiyya ta fitar, dukkanin waɗanda suka ji raunuka zasu samu Kimanin Naira miliyan 26.5, a yayinda iyalan waɗanda suka rasu zasu samu Kimanin Naira miliyan 53.1 kowanen su.
Zubairu Adamu, Babban yayan wanda ya rasu Shu’aibu Adamu daga Ƙaramar Hukumar Kubau, da wani Ibrahim Sani, wanda yace yaji raunuka a kafaɗar sa, sunyi kira ga Gwamna Nasir El-Rufa’i ya shiga tsakani.
Zubairu ya shaidawa Manema labaru cewa, marigayi yayan sa, yace ya mutu yabar mata biyu da ƴaƴa guda 10 wanda har yanzu basu samu diyyar ba, yana mai cewa sun rubuta takarda ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa domin tunatar wa, amma basu ce komai ba.
A lokacin da aka tuntuɓe shi mai kula da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa dake Kaduna Mrs Hannatu Zaiylani, tace chekin kuɗin daya fito a shekarar 2018 yazo amma da sunan mamacin, mai makon ɗan uwa