boko haram

Shekau Ya Gargadi ‘Yan Shi’a Da Darika A Sabon Bidiyo

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya gargadin shugaban Sojoji Laftanar Janar Tukur Burutai da ya daina kurarin cewa sun kawo karshensu.

Idan zaku iya tunawa Burutai ya ce tuni suka kawo karshen ‘yan ta’addan Boko Haram domin kuwa Boko Haram ba su rike da kowanne yanki a Nijeriya. Inda Shekau ya ce wannan zancen karya ne kawai Burutai yake yi.

Sannnan har wala yau  Shekaru ya gargadi jagoran mabiya shi’a a Nijeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da kuma mabiya darikar Tijjaniyyah karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Bauchi. Sannan ya ce suma al’ummar jihar Kano da Kaduna su shiga taitayinsu domin kuwa suna cikin hadari.

Har wala yau Shekau ya ce gargadi shugaban kasa Buhari da ka da ya sake ya sake dawo wa Maiduguri, ida ya sake ya sake dawo wa, to ‘yan Boko Haram tuni suka mamaye Arewa maso gabashin kasarnan, kuma idan ya dawo za sui ya kai wa shugaban kasar hari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *